Ezekiel 31:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَاڧِ دَغَ أَلْعُمَّ مَرَرْ تَوْسَيِ ڢِيٜىٰدَ سَوْرَنْ أَلْعُمَّيْ سُنْ سَارٜىٰشِ ڧَسَا، سُنْ بَرْشِ؞ رَسَّنْسَ سُنْ ڢَاطِ عَكَنْ تُدَّنْ دَسُكٜىٰ ثِكِنْ ݣُورُرُوَ، مَنْيَنْ رَسَّنْسَ سُنْ كَكَّرْيَ سُنْ ڢَاطِ أَ هَنْيُواْيِنْ دَ ضُوَيٜىٰ سُكٜىٰبِے؞ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دُونِيَا سُنْ تَاشِ دَغَ إِنُوَرْسَ، سُنْ بَرْشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Baƙi mafi bantsoro daga cikin al'ummai sun sare shi, sun bar shi. Rassansa sun faɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka, rassansa kuma sun kakkarye, sun faɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan mutanen duniya sun tashi daga inuwarsa, sun bar shi.