Ezekiel 31:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، أَ رَانَرْ دَ عَكَ غَنْ‌غَرَرْ دَشِ ذُوَا وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو، نَسَا ظُرْڢِنْ يَيِ مَكُواْكِنْسَ؞ نِے نَا ڟَيْ دَ كُواْغُنَنْسَ، نَا كُمَسَا ضُوَ مَيْ غُدُ يَڟَيَ؞ نَسَا لٜىٰبَنُوانْ ثِكِنْ دُهُ سَبُواْدَ بَڧِنْ ثِكِ، كُمَ دُكَنْ عِتَتُوَنْ كُرْمِ سُنْ بُوشٜىٰ سَبُواْدَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Allah ya ce, “A ranar da ya gangara zuwa lahira, na sa zurfi ya rufe shi, ya yi makoki dominsa. Na tsai da kogunansa, yawan ruwansa ya ƙafe. Na sa Lebanon ta yi duhu saboda shi. Dukan itatuwan jeji kuwa sun yi yaushi saboda shi.