Ezekiel 31:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَسَا أَلْعُمَّيْ سُكَيِ ضَوَرْ جِكِے سَبُواْدَ ڧَارَرْ ڢَاطُوَرْسَ، سَعَدَّ نَجٜىٰڢَرْ دَشِ ثِكِنْ وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو، تَرٜىٰدَ وَطَنْدَ سُكَ غَنْ‌غَرَ ذُوَا ثِكِنْ رَامِنْ مَتَتُّو؞ دُكَنْ عِتَتُوَنْ عَيْدَنْ دَ ذَاٻَٻُّنْ عِتَتُوَ نَ لٜىٰبَنُوانْ مَڢِے ݣَوْ، وَطَنْدَ دُكَنْسُ سُنْ ڧُواْشِ دَ ضُوَ، سُنْ سَامِ تَعَظِيَّ عَثِكِنْ دُونِيَرْ ذَمَنْ مَتَتُّو سَعَدَّ سُكَغَ إِتَاثٜىٰنَّنْ تَرٜىٰدَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Al'ummai suka yi rawar jiki saboda amon faɗuwarsa, sa'ad da na jefar da shi cikin lahira tare da waɗanda suke gangarawa zuwa cikin kabari. Dukan itatuwan Aidan da itatuwa mafi kyau na Lebanon waɗanda suka ƙoshi da ruwa, sun ta'azantu a lahira.