Ezekiel 31:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُو كُمَ سُكَ غَنْغَرَ تَرٜىٰ دَشِ ذُوَا وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو، وُرِنْ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ دَ تَكُواْبِے، تَرٜىٰدَ وَطَنْدَ سُكَ حَطَكَيْ دَشِ، وَتُواْ أَلْعُمَّنْ دَ سُكَيِ ذَمَنْسُ عَثِكِنْ إِنُوَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Su kuma suka gangara tare da shi zuwa lahira, suka tarar da waɗanda aka kashe da takobi, wato waɗanda daga cikin al'ummai suka yi zama a inuwarsa.