Ezekiel 31:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi. “ ‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹وَنٜىٰ إِتَاثٜىٰ نٜىٰ عَثِكِنْ عِتَتُوَنْ عَيْدَنْ يَنَ كَمَ دَكَيْ ثِكِنْ غِرْمَ دَ دَرَجَ؟ حَڧِيڧَ ذَاعَ غَنْ‌غَرَرْ دَكَيْ ذُوَا وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو تَرٜىٰدَ عِتَتُوَنْ عَيْدَنْ؞ ذَاكَ ݣُونْتَ تَرٜىٰدَ مَرَسَ سَنِنْ اللَّهْ دَ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ دَ تَكُواْبِے؞ « ‹ڢِرْعَوْنَ كٜىٰنَنْ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْسَ؞ نِے عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir'auna ke nan, da dukan jama'arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”