Ezekiel 32:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan sa mutane da yawa su giggice saboda abin da ya same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa’ad da na kaɗa takobina a gabansu. A ranar fāɗuwarka kowannensu zai yi rawar jiki a kowane lokaci saboda ransa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْسَا ڧَبِيلُ دَيَوَ سُرَسَ أَبِنْ ڢَطَا عَكَنْكَ؞ سَرَاكُنَ كُمَ سُيِ ضَوَرْ جِكِے سَبُواْدَكَيْ، سَعَدَّ نَكَطَ تَكُواْبِنَ أَغَبَنْسُ؞ أَ رَانَرْ ڢَاطُوَرْكَ، كُواْوَنّٜىٰنْسُ ذَيْ يِتَرَوَرْ جِكِے، كُواْوَ كُمَ ذَيْ يِتَكَنْسَ دُواْمِنْ رَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Al'ummai da yawa za su gigice saboda abin da zai same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa'ad da na kaɗa takobi a gabansu. A ranar faɗuwarka za su yi rawar jiki a kowane lokaci, kowa saboda ransa.”