Ezekiel 32:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، تَادَ وَاڧَرْ مَكُواْكِ دُواْمِنْ ڢِرْعَوْنَ سَرْكِنْ مَصَرْ، كَثٜىٰ، « ‹كَيْ كَا مَيْدَ كَنْكَ ذَاكِ نٜىٰ عَثِكِنْ أَلْعُمَّيْ، عَمَّا كَيْ كَمَ دَ دُواْدُواْ مَيْ صِڢَّرْ مَثِيجِ نٜىٰ عَثِكِنْ تٜىٰكُ؞ كَنَ تَجُجُّويَ ضُوً كُواْغُنَ، كَنَ تَدَمَ ضُوَ دَ ڧَڢَاڢُنْكَ، كَنَ تَݣُوٻَ ضُوً كُواْغُنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir'auna, Sarkin Masar, ka ce, ‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al'ummai, Amma kai kada ne a cikin ruwa. Ka ɓullo cikin kogunanka, Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka, Ka ƙazantar da kogunansu.’