Ezekiel 32:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga cikin kabari manyan shugabanni za su yi maganar Masar da abokanta su ce, ‘Sun gangara sun kuma kwanta da marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَنْيَ مَاسُ عِيَ يَاڧِ تَرٜىٰدَ مَاسُ تَيْمَكُوانْسُ ذَاسُ مَرَبْثٜىٰسُ، سُيِ مَغَنَ دَغَ وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو سُثٜىٰ، ‹أَيْ، سُنْ رِغَا سُنْ غَنْ‌غَرُواْ، غَاسُنَنْ ݣُونْثٜىٰ شِضُ، سُو مَرَسَ سَنِنْ اللَّهْ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ دَ تَكُواْبِے؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, ‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!’