Ezekiel 32:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
An yi mata gado a cikin matattu, tare da dukan jama’arta kewaye da kabarinta. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi. Domin tsoronsu ya bazu cikin ƙasar masu rai, suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami; an kwantar da su tare da waɗanda aka kashe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنْ شِرْيَ مَتَ غَدُواْ عَثِكِنْ مَتَتُّو تَرٜىٰدَ دُكَنْ جَمَعَرْتَ مَاسُيَوَ؞ كَبُرْبُرَنْسُ سُنَ كٜىٰوَيٜىٰ دَ عِتَ، أَنْكَكَّشٜىٰسُ دُكَ دَ تَكُواْبِے نٜىٰ؞ غَمَا دَا سُنْ يَطَ ذَمَنْ ڟُواْرُواْ عَدُونِيَرْ مَاسُ رَيْ، يَنْذُ سُنْ غَنْغَرَ ذُوَا رَامِنْ مَتَتُّو تَرٜىٰدَ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
An shirya mata gado tare da matattu. Kaburburan dukan sojojinta suna kewaye. Dukansu marasa imani ne, waɗanda aka kashe da takobi, amma a dā sun yaɗa tsoro a duniya. Yanzu kuwa suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari. An tara su tare da waɗanda aka kashe.