Ezekiel 32:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Edom tana can, sarakunanta da dukan yerimanta; duk da ikonsu, sun kwanta tare da waɗanda aka kashe da takobi. Suna kwance tare da marasa kaciya, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ڧَسَرْ عٜىٰدُوامْ مَا تَنَ ثَنْ، سَرَاكُنَنْتَ دَ دُكَنْ شُوغَبَنِّنْتَ، وَطَنْدَ دُكْ دَ إِيكُوانْ دَسُكٜىٰ دَشِ أَدَا، سُنَ ݣُونْثٜىٰ تَرٜىٰدَ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ دَ تَكُواْبِے؞ سُنَ ݣُونْثٜىٰ تَرٜىٰدَ مَرَسَ سَنِنْ اللَّهْ دَ كُمَ وَطَنْدَ سُكَ غَنْغَرَ ذُوَا رَامِنْ مَتَتُّو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Edom kuma tana can tare da sarakunanta da dukan shugabanninta masu iko, Suna kwance tare da waɗanda aka kashe da takobi, marasa imani, masu gangarawa zuwa cikin kabari.