Ezekiel 32:30 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Dukan yerima arewa da dukan Sidoniyawa suna can; sun gangara tare da waɗanda aka kashe cikin kunya duk da tsoron da suka haddasa ta wurin ikonsu. Sun kwanta tare da marasa kaciya tare da waɗanda aka kashe da takobi suna kuma shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دُكَنْ سَرَاكُنَنْ أَرٜىٰوَ سُنَ ثَنْ، دُكَنْسُ دَ دُكَنْ سِدُواْنِيَاوَا، ثِكِنْ كُنْيَا سُنْ غَنْ‌غَرَ تَرٜىٰدَ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ، دُكْ دَ ذَمَنْ ڟُواْرُوانْ دَ سُكَسَا وَمُتَنٜىٰ أَدَا سَبُواْدَ إِيكُوانْسُ؞ يَنْذُ سُنَ ݣُونْثٜىٰ تَرٜىٰدَ مَرَسَ سَنِنْ اللَّهْ وَطَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ دَ تَكُواْبِے، سُنْ شَا كُنْيَا تَرٜىٰدَ وَطَنْدَ سُكَ غَنْ‌غَرَ ذُوَا رَامِنْ مَتَتُّو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Dukan shugabannin arewa suna can, da dukan Sidoniyawa. Da kunya, suna gangarawa tare da waɗanda aka kashe, ko da yake a dā sun haddasa tsoro saboda ikonsu. Yanzu suna kwance tare da marasa imani waɗanda aka kashe da takobi. Suna shan kunya tare da waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.