Ezekiel 33:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka, ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen ƙasarka, ‘Adalcin adali ba zai cece shi sa’ad da ya ƙi yin biyayya ba, kuma muguntar mugu ba za tă sa ya fāɗi sa’ad da ya juya daga gare ta ba. Adali, in ya yi zunubi, ba za a bari yă rayu saboda adalcinsa na dā ba.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، سَيْ كَڢَطَا وَمُتَنٜىٰنْكَ ثٜىٰوَ أَدَلْثِنْ مَيْ أَدَلْثِے بَذَيْ كُٻُتَرْ دَشِيبَ، سَعَدَّ يَيِ ذُنُوبِنْ غَنْغَنْثِ؞ مُغُنْتَارْ مُوغُ كُمَ بَذَاتَ سَا يَمُتُبَ عِدَنْ يَا جُويُواْ دَغَ مُغُنْتَارْسَ؞ مَيْ أَدَلْثِے كُوَ عِدَنْ يَا يِ ذُنُوبِ، أَدَلْثِنْسَ نَدَا بَذَيْسَا يَرَايُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.