Ezekiel 33:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka faɗa musu wannan, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa muddin ina raye, waɗanda aka rage a kufai za su fāɗi ga takobi, waɗanda suke bayan gari kuwa namun jeji za su cinye su, waɗanda suke a mafaka da kogwannin duwatsu annoba za tă kashe su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ڢَطَا مُسُ كَثٜىٰ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، نَا ضَنْڟٜىٰ دَ رَيْنَ ثٜىٰوَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ أَوُرَارٜىٰنْ دَ عَكَ لَلَتَرْ، ذَاعَ كَشٜىٰسُ دَ تَكُواْبِے؞ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ أَ ڢِيلَيٜىٰ، ذَنْبَادَسُو غَ نَمُواْمِنْ دَاجِ سُثِنْيٜىٰسُ؞ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ثِكِنْ ٻُيَ عَكُواْڠُونِّ كُمَ، بَلَعِ ذَيْ كَشٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ka faɗa musu, ‘Ubangiji ya ce, “Hakika, waɗanda suke a wuraren da aka lalatar, za a kashe su da takobi, wanda kuma yake a saura zan sa namomin jeji su cinye shi. Waɗanda kuma suke cikin kagara, da kogwannin duwatsu, annoba za ta kashe su.