Ezekiel 33:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ مَيْ ڟَرُوانْ يَغَ تَكُواْبِے يَنَ ذُوَا، بَيْ بُوسَ ڧَهُوانْ دُواْمِنْ يَڢَطَكَرْ دَ مُتَنٜىٰنْ بَ، حَرْ تَكُواْبِنْ يَذُواْ يَكَشٜىٰ وَنِ دَغَ ثِكِنْسُ، مُتُمِنَّنْ دَ عَكَ كَشٜىٰ يَمُتُ سَبُواْدَ لَيْڢِنْسَ نٜىٰ، عَمَّا ذَنْ نٜىٰمِ أَلْحَكِنْ جِنِنْسَ دَغَ حَنُّنْ طَنْ ڟَرُوانْ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.’