Ezekiel 34:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے كُوَ ذَنْ ڢِتَرْ دَسُو دَغَ سَوْرَنْ ڧَبِيلُ، إِنْ تَتَّارُواْسُ دَغَ ڧَسَاشٜىٰ، إِنْ كَٰوُاْسُ ثِكِنْ ڧَسَرْسُ؞ نِے دَكَيْنَ ذَنْ ثِيَرْ دَسُو عَكَنْ تُدَّنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، عَبَاكِنْ مَٻُٻُّغَرْ ضُوَ دَ كُمَ دُكَنْ وُرَارٜىٰنْ دَ مُتَنٜىٰ سُكٜىٰ دَ ذَمَ عَڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan fito da su daga cikin sauran al'umma, in tattaro su daga ƙasashe dabam dabam, in kawo su ƙasarsu, in yi kiwonsu a kan tuddan Isra'ila, kusa da maɓuɓɓugai, da cikin dukan wuraren da mutane suke zaune a ƙasar.