Ezekiel 34:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bai isa ba a ce kun yi kiwo a wuri mai kyau? Sai kun tattake sauran wurin kiwonku da ƙafafunku tukuna? Bai isa ba a ce kun sha ruwa mai tsabta? Sai kun kuma gurɓata sauran da ƙafafunku?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَغَنِنْكُ، ڧَنْڧَنِنْ أَبُ نٜىٰ كُيِ كِيوُاْ عَكَنْ لَاڢِيَيَّرْ ثِيَوَ؟ بَايَنْ حَكَ، سَيْ كُتَتَّكٜىٰ سَوْرَنْ ثِيَوَرْ دَ ڧَڢَاڢُنْكُ؟ سَعَدَّ كُنْ شَا ضُوَ مَيْ لَاڢِيَ، يَنَدَ ݣَوْ كُݣُوٻَ سَوْرَنْ ضُوً دَ ڧَڢَاڢُنْكُ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ganinku abu mai kyau ne, bayan da kun yi kiwo a makiyaya mai kyau, sa'an nan ku tattake sauran makiyayar da ƙafafunku? Sa'ad da kuka sha ruwa mai kyau, sai kuma ku gurɓata sauran da ƙafafunku?