Ezekiel 36:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ba dominku ba ne, ya gidan Isra’ila da nake yin waɗannan abubuwa, amma saboda sunana ne mai tsarki, wanda kuka ɓata a cikin al’ummai inda kuka tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَبُواْدَ حَكَ، سَيْ كَڢَطَا وَ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، بَ دُواْمِنْكُ نٜىٰ، يَا غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، ذَنْيِ وَنِ أَبُبَ، عَمَّا دُواْمِنْ أَغِرْمَمَ سُونَنَ مَيْ ڟَرْكِے نٜىٰ وَنْدَ كُكَيِ بَنْظَ دَشِ عَثِكِنْ أَلْعُمَّيْ عِنْدَ كُكَتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Domin haka sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ba saboda ku ba ne, ya mutanen Isra'ila, zan yi wani abu, amma saboda sunana mai tsarki wanda kuka ɓata a wurin al'ummai inda kuka tafi.