Ezekiel 36:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa cikin kishina mai ƙuna na yi magana gāba da sauran al’ummai, da kuma gāba da Edom, gama da farin ciki da reni a zukatansu suka mai da ƙasata mallakarsu don su washe wuraren kiwonta.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، حَڧِيڧَ، نَيِ مَغَنَ ثِكِنْ ذَاڢِنْ كِيشِنَ نَيِنْ غَابَادَ سَوْرَنْ أَلْعُمَّيْ، مُسَمَّنْ دُكَنْ عٜىٰدُوامْ؞ أَلْعُمَّنَّنْ سُنْ طَوْكِ ڧَسَاتَ سُنْ مَيْدَ عِتَ أَبِنْ مَلَّكَرْسُ؞ دَ دُكَنْ ذُوثِيَارْسُ سُنَ ڢَضٍ ثِكِ دَ رٜىٰنِ ثٜىٰوَ سُنْ ݣُوشٜىٰ تَغَنِمَ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al'umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.’