Ezekiel 36:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ka yi annabci game da ƙasar Isra’ila ka kuma ce wa duwatsu da tuddai, wa kwazazzabai da kwaruruka, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al’ummai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دُواْمِنْ حَكَ ڢَا، سَيْ كَيِ أَنَّبْثِ عَكَنْ ڧَسَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كَثٜىٰ وَ مَنْيَ دَ ڧأَنَانً تُدَّيْ دَ مَٻُٻُّغَرْ ضُوَ دَ ݣُورُرُوَ كَثٜىٰ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، إِنَ يِنْ مَغَنَ ثِكِنْ ذَاڢِنْ كِيشِنَ سَبُواْدَ ثِكَكِّيَرْ ڧَوْنَرْ دَ نَكٜىٰ دَ عِتَ دُواْمِنْكُ، غَمَا كُنْ شَا ذَاغِ أَوُرِنْ أَلْعُمَّيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Domin haka ka yi wa ƙasar Isra'ila annabci, ka ce wa duwatsu, da tuddai, da kwazazzabai, da kwaruruka, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ga shi, na yi magana da kishina da hasalata saboda sun sha zargi wurin al'ummai.’