Ezekiel 37:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَثٜىٰ مِنِ «يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، وَطَنَّنْ ڧَسُسُوَ سُونٜىٰ دُكَنْ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ غَاشِ، سُنَ ثٜىٰوَ ‹ڧَسُسُوَنْمُ دُكْ سُنْ بُوشٜىٰ، مُنْ ڢِدَّ ذُوثِيَا، أَنْكَوَرْ دَمُو كَكَڢْ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’