Ezekiel 37:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan mai da su al’umma ɗaya a cikin ƙasar, a kan duwatsun Isra’ila. Za a kasance da sarki guda a kan dukansu ba za su ƙara zama al’ummai biyu ko su rabu su zama masarautai biyu ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ مَيْدَسُو أَلْعُمَّ طَيَ عَثِكِنْ ڧَسَرْ عَكَنْ مَنْيَنْ تُدَّنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ سَرْكِے طَيَ ذَيْ يِمُلْكِنْسُ دُكَ، بَذَاسُ ڧَارَ ذَمَ أَلْعُمَّ بِيُبَ، بَكُوَ ذَاسُ ڧَارَ رَبُوَ سُذَمَ مُلْكِ بِيُ بَكُمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan maishe su al'umma guda a ƙasar Isra'ila. Sarki ɗaya zai sarauce su duka, ba za su ƙara zama al'umma biyu ba, ba kuwa za su ƙara zama masarauta biyu ba.