Ezekiel 38:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَثٜىٰ «ذَنْ هَوْرَ إِنْ يَاڧِ ڧَسَرْدَ غَرُرُوَنْتَ بَاسُدَ كَتَنْغَ؞ ذَنْ كُوَ يَاڧِ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ ثِكِنْ سَلَمَ، رَيْ أَ سَكٜىٰ، دُكَنْسُ سُنَ ذَمَ أَغَرُضُوً دَ بَاسُدَ كَتَنْغَ، بَاسُدَ ڧُواْڢُواْڢِ، بَاسُدَ سَنْدُنَنْ ڧَرْڢٜىٰ نَكُلّٜىٰ ڧُواْڢُواْڢِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ka ce, ‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da suke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,