Ezekiel 38:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ ذُواْ دُواْمِنْ إِنْݣُوشِ رَبُوانْ يَاڧِ، إِنْكُمَ ݣُوشِ أَرْزِڧِ، إِنْيِ يَاڧِ دَ وُرَارٜىٰنْدَ دَا سُكٜىٰ كُڢَيْ، عَمَّا يَنْذُ أَݣَويْ مُتَنٜىٰ عَثِكِ؞ ذَنْيِ يَاڧِ دَ جَمَعَرْ نَنْ دَ عَكَ تَتَّارَ دَغَ أَلْعُمَّيْ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ دَ مَلَّكَرْ شَانُو دَ أَرْزِڧِ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ ظَوْنٜىٰ أَڟَكِيَرْ دُونِيَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
don in washe su ganima, in fāda wa wuraren da aka ɓarnatar waɗanda ake zaune a cikinsu yanzu, in kuma fāɗa wa jama'ar da aka tattaro daga cikin al'ummai waɗanda suka sami shanu da dukiya, suna zaune a cibiyar duniya.’