Ezekiel 38:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ka ci gaba a kan mutanena Isra’ila kamar yadda girgijen yakan rufe ƙasa. A kwanaki masu zuwa, ya Gog, zan kawo ka, ka yi yaƙi da ƙasata, domin al’ummai su san ni sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinka a gabansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ ڢَاطَوَ جَمَعَتَ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ يَاڧِ، كَمَرْ يَدَّ غِرْغِجٜىٰ يَكٜىٰ دُهُنْتَ ڢُسْكَرْ ڧَسَا؞ عَكْوَانَكِے نَڧَرْشٜىٰ، ذَنْ كَٰوُاْكَ كَيِ يَاڧِ دَ ڧَسَاتَ أَعِدُوانْ أَلْعُمَّيْ؞ ذَاعَ نُونَ ڟَرْكِنَ تَوُرِنْ أَبِنْدَ ذَيْ ڢَرُ دَكَيْ، يَا غُواغْ؞ تَهَكَ دُكَنْ أَلْعُمَّيْ ذَاسُ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.”’