Ezekiel 39:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za su yi wahalar zuwa jeji don neman itacen hura wuta ba, domin za su yi amfani da makamai don hura wuta. Za su kuma washe waɗanda suka washe su ganima, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاسُ شَا وَهَلَرْ نٜىٰمَنْ إِتَاثٜىٰ هُورَ وُتَادَغَ دَاجِ بَ، كُواْ سُسَارٜىٰ إِتَاثٜىٰ دَغَ كُرْمِبَ، غَمَا ذَاسُيِ تَهُورَ وُتَادَ كَايَنْ يَاڧِنْ؞ ذَاسُ ݣُوشِ كَايَ دَغَ وُرِنْ وَطَنْدَ دَا سُكَ ݣُوشٜىٰ دَغَ وُرِنْسُ، سُݣُوشِ رَبُوانْ يَاڧِ دَغَ وُرِنْ وَطَنْدَ دَا سُكَ ݣُوشٜىٰ دَغَ وُرِنْسُ؞ نِے عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za su yi wahalar zuwa jeji don nemo itacen wuta ba, gama za su yi ta hura wuta da makaman. Za su washe waɗanda suka washe su a dā, ni Ubangiji na faɗa.