Ezekiel 39:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Za a ɗauki mutane kullum don tsabtacce ƙasar. Waɗansu za su ratsa ƙasar, ƙari da waɗannan, waɗansu za su binne gawawwakin da suka ragu a ƙasar. A ƙarshen watanni bakwai ɗin za su fara bincikensu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَڧَرْشٜىٰنْ وَتَنِّ بَݣَويْ طِنْ، ذَاعَ كٜىٰٻٜىٰ مَظَا وَطَنْدَ ذَاسُيِ وَتَنِّ بَݣَويْ سُنَ تَبِنْ كُواْعِنَ عَڧَسَرْ سُنَ بِنْثِكَ، دُواْمِنْ سُبِنّٜىٰ دُكَنْ غَوَوَّكِنْ سُواْجُواْجِنْ دَ سُكَذُواْ يَاڧِ سُكَ مُتُ عَڧَسَرْ؞ تَهَكَ ذَاعَ ڟَبْتَثٜىٰ ڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko'ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta.