Ezekiel 39:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Al’ummai kuma za su san cewa mutanen Isra’ila sun tafi zaman bauta saboda zunubinsu, domin sun yi rashin aminci gare ni. Saboda haka na kawar da fuskata daga gare su na miƙa su ga abokan gābansu, suka kuwa mutu ta takobi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْعُمَّيْ ذَاسُسَنِ مُتَنٜىٰنْ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُنْ تَڢِے بَوْتَا سَبُواْدَ لَيْڢِنْسُنٜىٰ، غَمَا سُنْثِ أَمَانَتَ؞ شِيَسَا نَٻُواْيٜىٰ ڢُسْكَتَ دَغَ غَرٜىٰسُ، نَكُمَ بَادَسُو أَ حَنُّنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْسُ، دُكَنْسُ كُوَ عَكَ كَشٜىٰسُ دَ تَكُواْبِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Al'ummai kuma za su sani an kai jama'ar Isra'ila zaman bautar talala saboda muguntarsu, domin sun yi mini ha'inci, ni kuwa na kawar da fuskata daga gare su, na bashe su a hannun abokan gābansu, suka ci su da yaƙi.