Ezekiel 39:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Sa’an nan waɗanda suke zama a garuruwan Isra’ila za su fita su tattara makamai su hura wuta da su su kuma ƙone su, manya da ƙanana garkuwoyi, bakkuna da kibiyoyi, kulake da māsu. Shekara bakwai za su yi amfani da su don hura wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ عَثِكِنْ غَرُضُوً إِسْرَٰٓءِيلَ، ذَاسُ ڢِتُواْ سُتَتَّارَ كَايَنْ يَاڧِنْ، وَتُواْ غَرْكُوَ دَ رِيغُنَنْ ڧَرْڢٜىٰ نَيَاڧِ دَ بَكَ دَ كِبِيُواْيِ دَ سَنْدُنَ دَ مَاسُ؞ كَايَنَّنْ ذَاسُيِيَوَ، حَرْ ذَاعَيِ تَهُورَ وُتَادَسُو حَرْ شٜىٰكَرَا بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan su mazaunan biranen Isra'ila za su tattara makaman mutane, wato garkuwoyi, da bakuna, da kibau da kulake, da māsu, su yi ta hura wuta da su, har ya kai shekara bakwai.