Ezekiel 40:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya auna nisan da take daga hanyar shiga da take ƙasa-ƙasa daga ciki zuwa waje na filin ciki; ya kai kamu ɗari a gefen gabas haka ma yake a gefen arewa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَ عَوْنَ نِيسَنْ ڢِيلِنْ دَيَكٜىٰ ڟَكَانِنْ ڧُواْڢَ تَوَجٜىٰ دَ ڧُواْڢَ تَثِكِ، كَمُ طَرِے طَيَ نٜىٰ وَجٜىٰنْ غَبَسْ، حَكَ يَكٜىٰ كُمَ وَجٜىٰنْ أَرٜىٰوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya auna nisan da yake tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da take ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.