Ezekiel 40:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tagoginta, shirayinta da siffofin itatuwan dabinon da aka yi zāne-zānen adonta duk girmansu ɗaya ne da na ƙofar da take fuskantar gabas. Ɗakin shiga shi ma ya fuskanci filin yana kuma da matakai bakwai waɗanda suka bi zuwa ƙofar shiga, da shirayinta ɗaura da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غِرْمَنْ تَغُواْغِنْدَ نَذَوْرٜىٰنْ غِدَنْ، أَنْيِ أَدُوانْ صِڢَّرْ عِتَتُوَنْ دَبِينُواْ إِرِ طَيَ دَ نَڧُواْڢَرْ دَتَكٜىٰ ڢُسْكَنْتَرْ غَبَسْ؞ أَݣَويْ مَتَاكَلَنْ هَوَ بَݣَويْ ذُوَا وُرِنْ، ذَوْرٜىٰ كُوَ يَنَ ثَنْ ثِكِ يَنَ كُمَ ڢُسْكَنْتَرْ ڢِيلِ نَهَيْكَلِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Girman tagoginta, da na shirayin, da na siffar itatuwan dabinon da aka zana iri ɗaya ne da na ƙofar da ta fuskanci gabas. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki.