Ezekiel 40:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya kai ni gefen kudu, na kuma ga ƙofa tana fuskantar kudu. Ya auna madogaranta da shirayinta, dukansu girmansu ɗaya ne kamar sauran ƙofofi biyun.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَكَيْنِ وَجٜىٰنْ كُدُ، سَيْ نَغَ وَتَ ڧُواْڢَ أَوَجٜىٰنْ كُدُ؞ يَأَوْنَ غِنْشِڧِنْتَ دَ ذَوْرٜىٰنْتَ، غِرْمَنْسُ دَيْدَيْنٜىٰ دَ نَسَوْرَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma kai ni wajen kudu, sai kuma ga wata ƙofa. Ya auna ginshiƙanta da shirayinta. Girmansu ɗaya ne, kamar na sauran.