Ezekiel 40:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ɗakunanta, bangayenta da shirayinta duk girmansu iri ɗaya ne kamar sauran. Hanyar shiga da shirayinta suna da tagogi duk a kewaye. Tsawon hanyar shiga kamu hamsin ne, fāɗinta kuma kamu ashirin da biyar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ نَنْ كُمَ، أَݣَويْ طَكُنَنْ مَاسُ غَادِ دَ غِنْشِڧَنْ ڧُواْڢَرْ دَ كُمَ ذَوْرٜىٰ، غِرْمَنْسُ كُوَ دَيْدَيْنٜىٰ دَ نَسَوْرَنْ؞ أَݣَويْ كُمَ تَغُواْغِ كٜىٰوَيٜىٰ أَطَكُنَنْتَ دَ كُمَ أَ ذَوْرٜىٰنْتَ؞ ڟَوُانْ ثِكِنْ ڧُواْڢَرْ كَمُ حَمْسِنْ نٜىٰ، ڢَاطِنْسَ كُمَ كَمُ عَشِرِنْ دَ بِيَرْ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka nan kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu daidai yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.