Ezekiel 40:42 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu don hadayun ƙonawa, tsawon kowanne kuwa kamu ɗaya da rabi ne, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya. A kansu ne a kan ajiye kayan yanka hadayun ƙonawa da kuma sauran hadayu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَݣَويْ كُمَ تٜىٰبُرَ حُطُ وَطَنْدَ عَكَ سَسَّڧَ دَغَ دُوڟٜىٰ دُواْمِنْ أَ شِرْيَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، ڟَوُانْ كُواْوَنّٜىٰنْسُ كَمُ طَيَ دَ رَبِے، ڢَاطِنْ كُواْوَنّٜىٰنْسُ كُمَ كَمُ طَيَ دَ رَبِے نٜىٰ؞ أَ نَنْ ذَاعَ أَجِيٜىٰ كَايَنْ يَنْكَ دَبُّواْبِنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا دَ نَسَوْرَنْ هَدَايُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka.