Ezekiel 40:48 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya kawo ni shirayin haikalin ya kuma auna madogaran shirayin; fāɗinsu a kowane gefe kamu biyar-biyar ne. Fāɗin mashigin kamu goma sha huɗu ne, bangayenta kuma kamu uku-uku ne a kowane gefe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَبِے دَنِے ذُوَا ذَوْرٜىٰ نَهَيْكَلِنْ؞ يَكُمَ عَوْنَ غِنْشِڧَنْ ذَوْرٜىٰنْ، يَسَامِ كَمُ بِيَرْ نٜىٰ عَتَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ؞ ڢَاطِنْ ڧُواْڢَرْ كُوَ كَمُ غُواْمَشَا حُطُ نٜىٰ، ڟَوُانْ بَنْغُواْ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْ ڧُواْڢَرْ، كَمُ عُكُنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma kai ni a shirayin Haikalin. Ya auna ginshiƙan shirayin, kamu biyar ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar kuwa kamu uku ne a kowane gefe.