Ezekiel 40:49 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Fāɗin shirayin kamu ashirin ne, kamu goma sha biyu kuma daga gaba zuwa baya. A kan kai samansa ta wurin hawan matakai, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe na madogaran.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڟَوُانْ ذَوْرٜىٰنْ يَكَيْ كَمُ عَشِرِنْ، ڢَاطِنْسَ كُمَ كَمُ غُواْمَشَا بِيُ نٜىٰ؞ أَݣَويْ مَتَاكَلَنْ هَوَ غُواْمَ دُواْمِنْ هَوْرَ ذُوَا ذَوْرٜىٰنْ؞ أَݣَويْ كُمَ غِنْشِڧَيْ عَتَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْ غِنْشِڧَنْ ذَوْرٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tsawon shirayin kamu ashirin ne, faɗinsa kuwa kamu goma sha ɗaya. Akwai matakan hawa, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe.