Ezekiel 41:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Faɗin ƙofar shiga kamu goma ne, fāɗin bangaye a kowane madogararta kamu biyar-biyar ne. Ya kuma auna wuri mai tsarkin da yake waje; tsawonsa kamu arba’in fāɗinsa kuma kamu ashirin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢَاطِنْ حَنْيَرْ ڧُواْڢَ، كَمُ غُواْمَنٜىٰ؞ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ نَڧُواْڢَرْ أَݣَويْ بَنْغُواْ مَيْ ڟَوُاْ كَمُ بِيَرْ؞ سَيْ يَ عَوْنَ ڟَوُانْ بَبَّنْ طَاكِنَّنْ، كَمُ أَرْبَعِنْ نٜىٰ، ڢَاطِنْسَ كُمَ كَمُ عَشِرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Fāɗin ƙofar kamu goma ne. Madogaran ƙofar kamu biyar ne a kowane gefe. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu arba'in ne faɗinsa kuma kamu ashirin ne.