Ezekiel 41:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙofofin wuri mai tsarki da yake waje an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangayen, akwai kuma rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَڧُواْڢُواْڢِنْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے عَكَيِ ذَانِنْ صِڢَّرْ حَلِتَّ مَيْ ڢِكَڢِكِ دَ نَ إِتَاثٜىٰنْ دَبِينُواْ إِرِ وَنْدَ عَكَ ذَانَ عَكَنْ دُكَنْ بَنْ‌غُواْ؞ أَݣَويْ كُمَ رُمْڢَرْ دَ عَكَيِ دَ كَتَكُواْ أَغَبَنْ ذَوْرٜىٰنْ عَتَوَجٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ƙofofin Haikalin an zāna siffofin kerubobi da na itatuwan dabino kamar yadda aka zāna a bangon Haikalin. Akwai rumfar da aka yi da itace a gaban shirayin waje.