Ezekiel 41:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya shiga wuri mai tsarki da yake can ciki ya auna madogarar ƙofar shigar; fāɗin kowanne kamu biyu ne. Faɗin ƙofar shigan kamu shida ne, fāɗin bangayen a kowane gefenta kamu bakwai-bakwai ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَوُثٜىٰ تَثِكِنْ بَبَّنْ طَاكِنْ ذُوَا ڧُواْڢَ تَڧَرَمِنْ طَاكِ عَثَنْ ثِكِ؞ يَكُمَ عَوْنَ بَنْ‌غُوانْدَ يَرَبَ بَبَّنْ طَاكِ دَ ڧَرَمِنْ طَاكِ نَثِكِ، كَوْرِنْسَ كَمُ بِيُ نٜىٰ؞ ڢَاطِنْ ڧُواْڢَرْ كُمَ كَمُ شِدَنٜىٰ؞ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ نَڧُواْڢَرْ، أَݣَويْ بَنْ‌غُواْ مَيْ ڟَوُاْ كَمُ بَݣَويْنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya shiga ɗaki na can ciki, ya auna madogaran ƙofar, ya sami kamu biyu biyu. Tsayin ƙofar kuma kamu shida ne. Faɗin ƙofar kamu bakwai ne.