Ezekiel 41:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ɗakunan da suke gefe masu hawa uku ne, wani bisa wani, guda talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da bangayen haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon haikalin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَكُنَنْ دَسُكٜىٰ أَغٜىٰڢٜىٰنْ هَيْكَلِنْ، أَنْ‌غِنَسُ هَوَ عُكُنٜىٰ كَمَرْ تَمَتَاكَلَ؞ عَكُواْوَثٜىٰ هَوَ أَݣَويْ طَكُنَ تَلَاتِنْ أَجٜىٰرٜىٰ؞ تُوشٜىٰنْ كُواْوَثٜىٰ هَوَ تَطَكُنَنْ، عَكَ كَڢَ شِ عَكَنْ وَنْدَ يَكٜىٰ ڧَرْڧَشِنْسَ، يَدَّ كَدَ أَ حَطَ طَكُنَنْ دَ جِكِنْ بَنْ‌غُوانْ هَيْكَلِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ɗakunan benaye ne masu hawa uku. Akwai ɗakuna talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da Haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon Haikalin.