Ezekiel 41:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Faɗin ɗakunan da suke gefe kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. Ginin da aka yi kewaye da haikalin ya yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, don haka ɗakunan suka yi ta ƙara fāɗi yayinda suka ƙara bisa. Akwai mataki daga ɗaki na ƙasa zuwa ɗaki na bisa ta hanya hawa ɗaki na tsakiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢَاطِنْ كُواْوَثٜىٰ هَوَ يَڢِ ڢَاطِنْ وَدَّ تَكٜىٰ عَڧَرْڧَشِنْتَ؞ غِنِنَّنْ كٜىٰوَيٜىٰ دَ هَيْكَلِ، أَنْغِنَاشِ هَوَ هَوَ، يَدَّ طَكُنَنْ سُنْيِ تَڧَارَ ڢَاطِ حَرْ ذُوَا سَمَنْ غِنِنْ؞ أَنْ غِنَا وَتَ مَتَاكَلَ، تَمِيڧٜىٰ دَغَ ڧَسَا ذُوَا ڟَكِيَرْ غِنِنْ حَرْ ذُوَا سَمَنْ غِنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Faɗin ɗakunan yana ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, gama katangar da take kewaye da Haikali ta yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. A gefen Haikalin akwai matakan hawa. Don haka ana iya hawa daga ɗaki na ƙasa zuwa hawa na uku ta hanyar hawa na biyu.