Ezekiel 42:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da zarar firistoci suka shiga wuri mai tsarki, ba za su fita zuwa filin da yake waje ba sai sun tuɓe rigunan da suka yi hidima da su, gama waɗannan masu tsarki ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su kusaci wuraren da mutane suke.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ ڢِرِسْتُواْثِے سُكَ شِغَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے، بَذَاسُ ڢِتَ دَغَ ثِكِنْسَ ذُوَا ڢِيلِنْ دَيَكٜىٰ أَوَجٜىٰ بَ، سَيْ سُنْ تُوٻٜىٰ رِيغُنَنْ حِدِمَرْسُ، غَمَا وَطَنَّنْ رِيغُنَ مَاسُ ڟَرْكِے نٜىٰ؞ ذَاسُ سَا وَطَنْسُ رِيغُنَ كَاڢِنْ سُڢِتَ عِنْدَ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰ سُكٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da firistoci suka shiga Wuri Mai Tsarki, ba za su fita daga cikinsa zuwa farfajiyar da yake waje ba, sai sun tuɓe rigunan aikinsu, gama rigunan tsarkakakku ne. Za su sa waɗansu riguna kafin su tafi inda mutane suke.”