Ezekiel 43:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga lambatun da yake a ƙasa har zuwa ƙaramin mahaɗin da yake ƙasa wanda ya kewaye bagade, tsayinsa kamu biyu ne, fāɗinsa kuma kamu guda. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗin wanda ya kewaye bagade, zai zama kamu huɗu, fāɗinsa kuwa kamu ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَغَدٜىٰنْ يَڟَيَ عَكَنْ تُوشٜىٰ، يَنَ كُمَ دَ سَاشٜىٰ عُكُ؞ سَشٜىٰ نَڧَسَا، ڟَيِنْسَ كَمُ بِيُ نٜىٰ، ڢَاطِنْسَ كُمَ كَمُ طَيَ؞ سَشٜىٰ نَڟَكِيَ، ڟَيِنْسَ كَمُ حُطُ نٜىٰ، ڢَاطِنْسَ كُمَ كَمُ طَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tsayin bagaden zai zama kamu biyu daga gindinsa zuwa ƙaramin mahaɗinsa fāɗinsa kuma kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗi zai zama kamu huɗu, faɗinsa kuwa kamu ɗaya.