Ezekiel 43:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ka ɗibi jininsa ka zuba shi a ƙahoni huɗu na bagaden a gefen bisa da kuma kewaye da da’irar, ta haka za ka tsarkake bagaden ka kuma yi kafara dominsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ طِبَ دَغَ جِنِنْسَ، كَسَا عَكَنْ ڧَهُواْنِ حُطُ نَبَغَدٜىٰنْ، كَكُمَسَا عَكَنْ ݣُونَ حُطُ نَسَاشٜىٰ نَڟَكِيَ نَبَغَدٜىٰنْ دَ كُمَ عَكَنْ ڢِرَمْ دَيَكٜىٰ كٜىٰوَيٜىٰ دَ بَاكِنْسَ؞ تَهَكَ ذَاكَ ڟَبْتَثٜىٰ بَغَدٜىٰنْ، كَيِ هَدَايَرْ طَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ دُواْمِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da'irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa.