Ezekiel 43:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙarshen waɗannan kwanaki, daga rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama a kan bagade. Sa’an nan zan karɓe ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ وَطَنَّنْ ݣُونَكِے سُكَ وُثٜىٰ دَغَ رَانَ تَتَݣُوسْ ذُوَا غَبَ، ڢِرِسْتُواْثِے ذَاسُ مِيڧَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا دَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ؞ نِے كُوَ ذَنْ كَرْٻٜىٰكُ؞ نِے عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suka cika kwanakin nan bakwai, sa'an nan a kan rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayun ƙonawa da na salama a kan bagaden. Ni kuwa zan karɓe ku, ni Ubangiji Allah na faɗa.”