Ezekiel 43:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da suka sa madogarar ƙofarsu kusa da madogarar ƙofata, da katanga kawai a tsakanina da su, sun ɓata sunana mai tsarki ta wurin ayyukansu masu banƙyama. Saboda haka na hallaka su cikin fushina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْ ڧَظَنْتَرْدَ سُونَنَ مَيْ ڟَرْكِے سَعَدَّ سُكَ كَڢَ ڧُواْڢَرْ غِدَنْسُ كُسَدَ ڧُواْڢَتَ، سُكَ كُمَ كَڢَ ڢِرَمْ نَڧُواْڢَرْسُ كُسَدَ ڢِرَمْ نَوَ، بَنْ‌غُواْ نٜىٰ كَطَيْ يَرَبَ ڟَكَانِينَ دَسُو؞ سُكَ ڧَظَنْتَرْدَ سُونَنَ مَيْ ڟَرْكِے تَوُرِنْ أَيُّكَنْسُ نَبَنْ ڨَمَرْ دَسُكَ عَيْكَتَ؞ سَبُواْدَ حَكَ نَهَلَكَاسُ ثِكِنْ ڢُشِنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ko kuwa ta wurin sa dokin ƙofarsu kusa da dokin ƙofata, da kuma ta kafa madogaran ƙofarsu kusa da nawa, sai dai katangar da ta yi mana tsakani. Sun ɓata sunana mai tsarki da ayyukansu masu banƙyama, don haka na hallaka su saboda sun sa na husata.