Ezekiel 44:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَيَكٜىٰ لَوِيَاوَا سُكَيِ وَ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ حِدِمَ أَغَبَنْ غُمَكَنْسُ، سُكَ ذَمَ دَلِيلِنْ تُنْتُٻٜىٰنْسُ؞ سَبُواْدَ حَكَ، نِے عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ضَنْڟٜىٰ ثٜىٰوَ ذَاسُ غِرْبِے أَلْحَكِنْ لَيْڢِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu.