Ezekiel 44:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba za su yi kusa don su yi hidima kamar firistoci ko su zo kusa da abubuwana masu tsarki ko hadayuna mafi tsarki ba; dole su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاسُذُواْ كُسَدَنِے دُواْمِنْ سُيِ مِنِ حِدِمَ أَمَڟَيِنْ ڢِرِسْتُواْثِے بَ، كُواْ سُذُواْ كُسَدَ هَدَايُنَ مَاسُ ڟَرْكِے، وَتُواْ أَبُبُوَ مَڢِے ڟَرْكِيبَ؞ عَمَّا ذَاسُ شَا كُنْيَا سَبُواْدَ أَيُّكَنْسُ نَبَنْ ڨَمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.