Ezekiel 44:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Amma firistoci, waɗanda suke Lawiyawa kuma zuriyar Zadok waɗanda suka yi aminci ta wurin yin ayyukansu a wurina mai tsarki sa’ad da Isra’ilawa suka kauce daga gare ni, su ne za su zo kusa don hidima a gabana; za su tsaya a gabana don miƙa hadayun kitse da jini, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹عَمَّا ڢِرِسْتُواْثِے نَ عِيَلِنْ ظَدُواكْ نَظُرِيَرْ لَوِ، وَطَنْدَ سُكَيِ أَمِنْثِ ثِكِنْ حِدِمَرْ وُرِينَ مَيْ ڟَرْكِے سَعَدَّ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ كَوْثٜىٰ سُكَ بَرْ نِے، سُونٜىٰ ذَاسُذُواْ كُسَ سُيِ مِنِ حِدِمَ دُواْمِنْ سُمِيڧَ مِنِ كِڟٜىٰ دَ جِنِ نَهَدَايَ؞ نِے عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.