Ezekiel 44:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da suka fita daga haikali zuwa fili na waje inda mutane suke, sai su tuɓe rigunan da suka yi hidima da su su bar su a tsarkakan ɗakuna, su sa waɗansu riguna, don kada su tsarkake mutane ta wurin rigunansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْ سُڢِتَ ذُوَا ڢِيلِنْ وَجٜىٰ وُرِنْ دَ مُتَنٜىٰ سُكٜىٰ، ذَاسُ تُوٻٜىٰ رِيغُنَنْ دَ سُكَيِ حِدِمَ دَسُو، سُأَجِيٜىٰ أَطَكُنَ مَاسُ ڟَرْكِے؞ سَيْ سُسَا وَطَنْسُ رِيغُنَ دُواْمِنْ كَدَ رِيغُنَنْسُ مَاسُ ڟَرْكِے سُسَا سَوْرَنْ مُتَنٜىٰ سُذَمَ مَاسُ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.