Ezekiel 44:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹عِدَنْ أَنَ غَرْدَمَ سُونٜىٰ ذَاسُ ڟَيَ كَمَرْ أَلْڧَلَيْ، سُيِ شَرِيعَ سُيَنْكٜىٰ مَغَنَ بِسَغَ عُمَرْنَيْنَ؞ ذَاسُ كِيَايٜىٰ كُواْيَرْوَاتَادَ ڧَٰعِدُواْدِنَ غَمٜىٰدَ دُكَنْ ڟَارِنْ بُكُكُوَنَ؞ ذَاسُ كُمَ كِيَايٜىٰ رَانَرْ هُوتُ تَمَكُواْ تَاوَ دَ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su zama masu raba gardama, za su yanke magana bisa ga doka. Za su kiyaye idodina bisa ga tsarinsu. Za su kuma kiyaye ranakun Asabar masu tsarki.